Wasanni: Dan Kwalambiya ya lashe gasar Tour de France | Zamantakewa | DW | 29.07.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Wasanni: Dan Kwalambiya ya lashe gasar Tour de France

A karon farko cikin tarihin gasar tseren kekuna ta Tour de France da ake yi kowacce shekara, wani dan kasar Kwalambiya ya lashe gasar.

Saurari sauti 09:55

A ranar Lahadi aka kammala gasar tseren kekuna ta Tour de France, inda a karon farko cikin tarihin gasar wani matashi dan shekaru 22 kacal dan kasar Kwalambiya mai suna Egan Bernal ya lashe. Bernal da ke zama mutun mafi karancin shekaru da ya taba lashe gasar ya kuma kafa bajintar zamowa dan kasar Kwalambiya na farko kana dan Latin Amirka na farko da ya taba lashe wannan shahararriyar gasar tseren kekuna ta Tour de France. A karshen gasar kungiyar Ineo ta Egan Bernal wanda ya lashe gasar ta samu tukuicin kudi kusan Euro dubu 800.

A gasar tseren motoci ta Formula One ta kasar Jamus ko kuma Grand Prix d'Allemagne, dan kasar Holland Max Verstappen na kamfanin Red Bull ne ya lashe gasa da ta gudana a birnin Hockenheim a yayin da dan kasar Jamus Sebastian Vettel na kamfanin Ferrari ya zo na biyu, sai kuma Daniil Kvyat na kamfanin Toro Rosso a matsayin na uku.