Wasanni: Bayern Munich ta tabbatar da matsayinta giwar Bundesliga | Zamantakewa | DW | 10.05.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Wasanni: Bayern Munich ta tabbatar da matsayinta giwar Bundesliga

Bayern Munich ta sake zama zakaran da Allah ya nufa da cara a gasar lig ta kwallon kafar Jamus makonni biyu kafin kawo karshen kakar wasannin Bundesliga na 2020-2021.

Wannan bajintar ta samu ne bayan da RB Leipzig ta fada tarkon Borussia Dortmund wacce ta doke ta da ci 3-2 a ranar Asabar, lamarin da ya sa Yaya-babba samun yawan maki da take bukata na zama gwarzuwa tun ma kafin ta yi wasanta da Borussia Mönchengladbach. Sai dai bai hana 'yan wasan Koci Hansi Flick daukar wasansu da Mönchengladbach da muhimmanci ba, tare da buga daya daga cikin mafi kyawun wasanninsu a kakar bana ba, inda tsuka zura kwallaye 6-0. Godiya ta tabbata ga dodon raga Robert Lewandowski wanda ya kara sabbin kwallaye uku a komarsa mai jimillar kwallaye 39. Alal hakika ma dai dan wasan gaban Bayern Munich ya kusa cimma tarihin da dan wasa Gerd Müller ya kafa a kakar 1971/1972, inda wanda ake wa lakabi da “Der Bomber” ya ci kwallaye 40 a shekara guda.

Ko ma dai ya zata kaya dai, Bayern Mucih na ci gaba da jan zarenta ba tare da ya tsinke mata ba, inda za ta ci gaba da zama jagora shekaru tara a jere, kuma sau 30 cikin tarihin Bundesliga na shekaru 58. Daidai da Mahadi mai dogon zamani na Bayern wato Thomas Müller mataimakin kyaftin na kungiyar.


"Samun lashe kambun zakaru sau tara a jere abin farin ciki ne! kuma da ni aka dama a duk wadannan shekaru. Ina mai matukar farin cikin samun wannan jikin, wannan shi ne abin da ya ba ni damar buga kwallon kafa a tsawon wannan lokaci. Abun mamaki ne. Kowace shekara muna gudanar da gagarumin aiki, kuma a kowace shekara muna samun kwarin gwiwar yin aiki da zuciya, amma kuma a kowace shekara muna samun ci gaba, muna da babbar tawaga. "


A kasan teburin Bundesliga kuwa, Cologne ta bi Freiburg har gida kuma ta lallasa  ta da ci 4-1, lamarin da ya sa ta sake dawowa matsayi na 17 da maki 29. Ita kuwa Bielefeld ta tashi 0-0 da Hertha Berlin, kuma tana a matsayi na 16. Haka ita ma Werder Bremen ta tashi 0-0 da Bayer Leverkusen. Koda Augsburg da ke a matsayi na 13 tare da maki 33 kawai, ba ta tsira daga gangarawa karamin lig ba. Hertha Berlin ce kawai ke cikin mafi kyawun matsayi don tana da wasa daya da ya rage mata.

Kungiyar mata ta Chelsea ta ci gaba da rike kambunta a matsayin zakarar kwallon kafar Ingila cikin sauki bayan da ta doke Reading

(5-0) a wasan makon karshe, lamarin da ya sa ta yi wa Manchester City wacce ta mamaye West Ham (1- 0) ratar maki biyu. Ita dai Chelsea ta kasance kungiya ta farko da ta cancanci shigar da rukuninta na maza da mata a shekara guda a gasar zakaru na kwallon kafar Turai. Sau daya kawai aka doke kungiyar mata ta Chelsea a wannan kaka, kuma ta gama da mafi kyawun tsaro don kwallaye 10 kawai aka zura mata, Yayin da ta yi wa takwarorinta zarra a fannin cin kwallo, inda ta ci kwallaye 69.

A rukunin maza na Premier Lig kuwa, Manchester United ta sake jinkirta bajintar takwararta ta City na zama zakaran kwallon kafa ta hanyar lashe wasa 3 da 1 da ta yi da Aston Villa ranar Lahadi a mako na 35. Wannan ya faru ne saboda 'yan wasan koci Pep Guardiola sun baras da wasansu da Chelsea da ta doke city da (2-1), a wasan da ke zama zakaran gwajin dafi na wasan karshe na neman cin kofin zakarun Turai da zai gudana a ranar 29 ga Mayu. A yanzu dai Manchester city na saman teburin Premier Lig da maki 80, yayin da manchester United ke biya mata baya da maki 70, Chelsea kuwa na a matsayi na uku da maki 64.

Gwamnatin Japan ta ce babu gudu babu ja da baya wajen shirya wasannin olympik tare da gudanar da su a watan Yuli mai zuwa a birnin Tokyo, duk da adawa da jama'ar kasar ke nunawa bisa dalilai na annobar corona. Wasu 'yan wasan kasar da suka taba kamuwa da covid-19 sama da 100 sun yi zanga-zangar adawa da wasannin Olympics a gaban Filin Wasanni na Tokyo. Sai dai Kwamitin Olympik na duniya da fadar mulki ta Tokyo tace suna ci gaba daukan matakai kiwon lafiya domin komai ya gudana salin alin. 

A karon farko tun lokacin da aka kirkiri jadawalin 'yan wasan Tennis mafi shahara a duniya a shekarar 1973, ba a sami Ba'amurke da ya kasance a cikin jeren mutane 30 mafi daraja na ATP ba. Maimakon haka Novak Djokovic na Sabiya ya kasance a matsayin gwani na gwanayen Tennis na duniya. Shi kuwa Daniil Medvedev na Rasha ya gaji matsayi na 2 a duniya daga Rafael Nadal na Spain, wanda aka fitar a wasan kusa da na karshe na Masters din Madrid. Dan Amirka na farko da ke da kyakkyawan matsaiyi shi ne Taylor Fritz wanda ya rasa maki, kuma ya samu kanshi a matsayi na 31. 

Wannan jadawalin ya nuna yadda Amirka ke fuskantar komabaya a fagen Tennis, alhali ita ce kasar da ta fi yawan gwarazan 'yan wasa na duniya irin su (Jimmy Connors, John McEnroe,  Andre Agassi, Andy Roddick da sauran su. Rabon Amirka ta sami matsayin gwani na gwanayen tennis na maza tun farkon 2004.

A yanzu dai, Bajamushe Alexander Zverev, wanda ya yi nasara a wasan karshe a ranar Lahadi a Madrid - ya karfafa matsayinsa na 6. Yayin da wanda ya sha kaye a Masters din madrid wato dan kasar Italiya Matteo Berrettini, ya tashi daga matsayi na 10 zuwa na 9 a duniya.