Wasan kwallon kafa tsakanin mata a Ghana | Zamantakewa | DW | 30.07.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Wasan kwallon kafa tsakanin mata a Ghana

Tun a 1991 wasan kwallon kafa ya fara samun karbuwa a zukatan matan kasar, duk da sabanin fahimta da suke fuskanta daga bangaren al'umma.

Al'ummar kasar Ghana, mutane ne masu kaunar wasannin kwallon kafa, ko da yake bayan nan an hakikance cewar wasanni na taimaka wa rayuwar wadanda suke yi ta hanyoyi da dama. Tun a shekarar 1991 ne wasan kwallon kafa ya fara karbuwa a zukatan mata a Ghana, duk da sabanin fahimta da suke fuskanta daga bangaren al'umma.

Yau ma dai kamar kullum, kungiyar wasan kwallon kafa ta mata zalla mai suna Ghana Police, suna gudanar da atisaye a wani filin wasa dake barikin 'yan sanda na unguwar Tesano, mai 'yar tazara daga tsakiyar Accra babban birnin kasar. Suna buga kwallo tsakaninsu bisa umarnin mai ba su horo Chris Dakey.

Burin zama wani abu a rayuwa

Wadannan 'yan wasa na da manufar da suke son cimma, manufar bata wuce buga wa manyan kungiyoyin wasannin kwallon kafa na mata ba. Haka kuma kowacce tana da labarin yadda aka yi ta tsinci kanta cikin wannan aiki.

Germany team coach Silvia Neid, center, walks in front of Germany's Birgit Prinz after Germany lost 0-1 the quarterfinal match between Germany and Japan at the Women’s Soccer World Cup in Wolfsburg, Germany, Saturday, July 9, 2011. (AP Photo/Jens Meyer)

Kwallon kafa mata dai ba sabon abu ba ne a kasashen Turai kamar Jamus

Priscilia Otchere, ta kasance kyaftin a kungiyar wasan kwallon kafa ta Ghana Black Maiden, kungiyar da ta wakilci kasar a gasar wasan kwallon kafa ta duniya ta mata 'yan kasa da shekaru 17 a kasar Azarbeijan, ta bayyana yadda ta fara buga wasan kwallon kafa.

"Wannan baiwa ce da Mahalicci Ya yi mini. Duk da cewa mahaifana ba sa so, shi ma bisa hujjar ba zan mayar da hankali kan ayyukan gida ba, ba kuma zan mayar da hankali a kan karatu ba, kamar yadda ake gani mafi yawan masu buga wasan kwallo ba su da wani ilimi mai zurfi. Lokacin da na samu kaina cikin wannan harka na ji zuciyata ta kadu a tashin farko, tun da dai ban iya ba, amma kuma Mahalicci Ya bani baiwa, da na ga 'yan uwana suna yi sai na fada wa zuciya cewar zan iya bugawa fiye da su."

Wannan 'yar wasa Priscilia dai ita ke rike da kambun marubuta harkokin wasanni rukunin mata na shekarar 2012 da 2013 a kasar Ghana, duk da cewa iyayenta ba sa so tun da farko ta shiga harkokin wasanni, yanzu haka ita ce ke daukar nauyin dukkanin 'yan uwanta da iyayen a hannu guda.

"Tsoho da gyatuma ta ba su da komai da za su iya kula da bukatu na, amma ina kallon kaina a matsayin abar alfahari da na fito daga gidan talauci, yanzu Allah Ya hore min abin da zan fitar da gidanmu daga kunci, kaga yanzu zan iya share wa iyayena hawaye."

Micahel Otchere dan uwa ne ga Priscilia, ya bayyana wahalar da 'yar uwarsa ta shiga sakamakon zabin shiga harkokin wasanni da ta yi a tashin farko.

"Nungua Priscilia yarinya ce mai kwazo, kuma maganar da nake maka yanzu ita ce ke dauke da nauyin gidanmu baki daya, abu ne mai matukar alfanu daukar harkar wasan kwallo kafa a matsayin abin yi, a yanzu tana samun dukkanin hadin kai da take bukata daga bangarenmu."

Kokarin shawo kan iyaye

Chris Dakey, shi ne mai horas da 'yan wasan kungiyar kwallon kafa da Priscilia ke bugawa wasa, ya ce akwai mata masu hazaka da dama a Ghana, sai dai shawo kan iyayensu shi ne aiki.

"Za su zo mini da matsaloli, amma a matsayi na mai horas da su, uba ne ni a gare su, dole na samu iyayensu kafa da kafa domin shawo kansu."

Babban tunanin wannan mai horaswa bai wuce fadakar da iyaye su bar 'ya'yansu domin shiga wannan sana'a ba, domin yana taimakawa wajen rage dogaro da 'ya'ya mata ke yi da wasu, hakan zai taimaka wajen rage manyan kaba'irai.

Mawallafa: Isaac Kaledzi / Garzali Yakubu
Edita: Mohammad Nasiru Awal