1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaJamus

Wariyar launin fata da talauci ne matsalolin baki a Jamus

Marcel Fürstenau Usman Shehu Usman/MAB
May 8, 2024

Wani bincike da aka gudanar a Jamus ya nunar da cewar Musulmi da 'yan asalin Asiya da bakar fata sun fi fuskantar barazanar talauci a kasar. Ko da masu ilimi mai zurfi na fiskatar tsaiko fiye da sauran jama'ar kasar.

https://p.dw.com/p/4fd05
Matalauta na shiga mummunan hali a loacin sanyin hunturu a Jamus
Matalauta na shiga mummunan hali a loacin sanyin hunturu a JamusHoto: Michael Gstettenbauer/IMAGO

Hakika matsalar wariyar launin fata ta yadu a Jamus. Amma wane sakamako na zahiri za ta iya haifarwa ga wadanda abin ya shafa? Klara Podkowik, masaniya da ke cibiyar nazarin ala'amuran baki da sajewarsu cikin al'umma ta duba irin wadanda lamari ya shafa, inda ta duba ko akwai alaka tsakanin wariyar da ake nunawa da kuma talauci. Ta ce: "Kusan 20% na matan Musulmai da muka zanta da su tun daga shekarar 2013 ne suka zo Jamus. Sun shigo ne daga Siriya da Afghanistan da sauran kasashe. Kuma an riga an san cewa 'yan gudun hijirar na fuskantar barazanar talauci saboda wahalar shiga sahun wadanda za a dauka aiki”.

Karin bayani: Talauci a Jamus

Matalauta na layi don samun abinci mai saukin farashi a wasu birane na Jamus
Matalauta na layi don samun abinci mai saukin farashi a wasu birane na JamusHoto: Frank Hoermann/SVEN SIMON/picture alliance

Tushen nazarin shi ne Hukumar Kula da Wariyar Jama'a ta kasa wanda Salikutluk ta dauki nauyin gudanarwa. Kamar yadda masaniyar ta ce: "Idan aka yi la'akari da kididdigar hukuma ko rahoton talauci da arzikin da gwamnatin tarayyar Jamus ke samu, yawancin talauci ya fi ritsawa da mutanen da ke da asalin hijira a kasar ta Jamus. Kuma wannan ya shafi har da wadanda suka samu takardun zama dan kasa kasa.”

Karin bayani:Masallatai a Jamus na fuskantar barazana

Binciken da aka yi ya gano cewa akasarin baki a Jamus ba wai basu da ilimi b ane, misali 33% mutanen da aka tambaya musamman Musulmi na da ilimin da ake bukata ko kuma sun kware a wanni fanni, amma sun fuskantar matsala wajen neman aiki, domin wasu jami'o'i da makarantun gaba da sakandare na kasar Jamus ba sa la'akari da shaidar karatun. A cewar Klara Podkowik, "Mutanen da ke da sunan Turkawa misali, suna da karancin damar gayyatar su zuwa bitar inda ake daukar aiki. Kuma tabbas wadannan bangarorin y akakmata a yi gyara a kai”

Karin bayani: Jamus: Cusa dokokin Musulumci a siyasa

Dalibai Musulmi daga Bangaladesh na haduwa don bikin sallah a Jamus
Dalibai Musulmi daga Bangaladesh na haduwa don bikin sallah a JamusHoto: Abu Sayem

Amma akwai bukatar samun ilimi a kasa ta asali da mutum ya fito don zai hanzarta shigar 'yan gudun hijira da sauran 'yan ci-rani cikin kasuwar kwadago ta Jamus. A wani bangaren kuma, wadanda suka yi karatu gabanin zuwansu kasar Jamus sun fi saurin koyon harshen Jamusanci, wanda ke zama babbar dama ta samun aiki cikin sauri.