Wani sabon rikicin ƙabilanci ya ɓarke a Darfur | Labarai | DW | 25.06.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Wani sabon rikicin ƙabilanci ya ɓarke a Darfur

An kashe mutane aƙalla 80 tun daga farkon watan Mayu a faɗan da ake gwabzawa tsakanin wasu ƙabilu biyu da ke Darfur a ƙasar Sudan

Ƙabilun na Gimir da Beni Halba na kabsa faɗa ne tun cikin watan Afrilun da ya gabata a garin Edd-Al-Fursan a kan rigingimu gonaki da filaye.

A farkon watan Mayu aƙalla mutane 80 suka mutu a faɗan wanda masu aiko da rahotannin suka ce an ƙone gidaje da dama. Ƙwararrun a kan sha'anin kare hakin hakin jama'a na MDD sun zargi gwamnatin Sudan da ƙara rurra wutar rikicin tsakanin ƙabilin biyu. Shugaban rundunar wanzar da zaman lafiya na MDD Ibn Chambas ya ce faɗan ya tilastawa mutane kamar dubu ɗari uku barin gidajensu tun daga farkon wannan shekara kawo yanzu.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman