Wani mutum ya kai hari da zarto a Switzerland | Labarai | DW | 24.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Wani mutum ya kai hari da zarto a Switzerland

Maharin ya kusa kai ne cikin ginin wata ma'aikata da ke kusa da wasu manyan shaguna da ke birnin Schaffhausen da ke arewacin kasar Switzerland, garin da ke kan iyaka da Jamus.

Maharin ya raunata mutane biyar inda biyu daga cikin mutanen ke cikin mummunan hali. Rahotannin da 'yan sanda suka bayar na cewa harin ba na ta'addanci ba ne. To sai dai yanzu 'yan sandan sun ce an kai ga gano maharin amma ba a tantance sunansa ba.

Tuni aka baza jami'an tsaro ta sama da kuma wasu ta kasa da nufin kare sauran al'umma, akwai jami'an gaggawa a wurin da abin ya faru wadanda ke ba da agaji ga mutanen da suka raunata daga harin an kuma bada umarnin ficewar mutane don killace yankin baki daya.