1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wani mutum ya harbe dalibai uku a Amirka

February 14, 2023

Mutimin ya kai harin ne da kimanin karfe biyu na safiyar Talata a gidan kwanan dalibai na jami'ar Lansing da ke yanmancin Amirka inda ya buda wuta kan daliban.

https://p.dw.com/p/4NRsC
USA East Lansing | Schüsse an der Michigan State University
Hoto: Jakkar Aimery/Detroit News/AP/picture alliance

Maharin bakar fata ya harbe dalibai uku har lahira tare da jikkata wasu biyar da aka kwantar a gadon asibiti kafin daga bisani ya ranta a na kare.

Sai dai bayan baza dariruwan jami'an 'yan sanda domin farautar maharin tare da yada hutunansa an tsinto gawarsa a kusa da inda ya kai harin shima ya kashe kansa bayan ya yi wannan aika-aika.

Tuni dai aka dakatar da harkoki a jami'ar tare da kiran dalibai kusan dubu 50 da ke karatu a ciki da kuma ma'aikata da su killace kansu.

A shekarun baya-baya nan dai ana dada samun karuwar kisa ta hanyar yin anfani da bindiga a kasar Amirka lamarin da ake alankantawa da bazuwar makamai a kasar inda aka kiyasta cewa magidanta biyu cikin uku a Amirka sun mallaki bindiga.