Wani kumbo ya tashi zuwa tashar sama ta ISS | Labarai | DW | 03.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Wani kumbo ya tashi zuwa tashar sama ta ISS

Kumbon zai kai kayan abinci da na'urorin zamani ga tashar sararin samaniya ta kasa da kasa ta ISS inda 'yan sama jannati ukku ke aiki

Wannan kumbo maras matuki ya tashi yau Juma'a zuwa wata tashar sararrin samaniya ta kasa da kasa mai suna ISS. Kumbon wanda aka harba shi daga wata tashar harba kumbo ta kasar Rasha ya yi nasarar tashi, bayan da a baya sa biyu yinkurin harba shi na gamuwa da cikas.

Kwanaki biyu ne dai kumbon mai dauke da ton ukku na kayan abinci da sabbin na'urorin aiki na zamani zai yi, yana tafiya cikin sararin samaniyar kafin a ranar lahadi mai zuwa ya isa masaukinsa da karfe bakwai da mintoci 13 agogon GMT, inda ma'aikatan tashar sararin samaniyar su ukku ke jiran sa.