1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wani jirgin soji na Kwango ya fadi

Abdourahamane Hassane
September 30, 2017

Wani jirgin sama na soji samfarin Antonov na rundunar sojojin Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango wanda wani dan kasar Rasha ke tukawa, ya tarwatse a gabashin birnin Kinshasa.

https://p.dw.com/p/2l1PV
Symbolbild - Antonov 12 - Militärflugzeug
Hoto: picture-alliance/AA/R. Netisov

Wata majiya soji ta ce jirgin da ya tashi daga garin Ndolo dauke da fasinja 20 zuwa 30 galibi sojoji da kuma makamai zuwa  garin Kivu a gabashin Kwango ya fadi a garin  N'sele da ke da nisan kilomta 100 daga Kinsasha. Kuma bisa ga dukkan alamu babu daya daga cikin fasinjan da ke cikin jirgin wanda ya tsira da ransa.