Wani jirgin sama na Aljeriya ya ɓace | Labarai | DW | 24.07.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Wani jirgin sama na Aljeriya ya ɓace

Kamfanin sufirin jiragen sama na Aljeriya ya ce, ya rasa samun bayyanai na tuntuɓa daga wani jirgin sama na fasinja, jun kadan bayan mintoci 50 ya tashi daga Ouagadougou zuwa birnin Algers.

Jirgin samfarin MD-83 wanda Aljeriya ta yi hayya daga wani kamafin na ƙasar Spain, na ɗauke da fasinja 116, kuma 50 daga cikinsu 'yan ƙasar Faransa ne. Jirgin wanda ya tashi da misalin ƙarfe ɗaya na daran jiya daga Ouagadougou yakamata ya isa a Algers a yau da ƙarfe huɗu na safe.

Sai dai wasu rahotannin da ke shigo mana yanzu na cewar ministan sufiri na Burkina Faso, ya ce jirgin ya canza hanya ne saboda mummunar yanayi. Kuma naurar hangen jiragen sama ta hangoshi a sararrin samaniyar ƙasar Mali.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu