Wani jirgin ruwa ya kife a tsibirin Kalymnos na Girka | Labarai | DW | 30.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Wani jirgin ruwa ya kife a tsibirin Kalymnos na Girka

Jirgin ruwan na ɗauke da 'yan ci rani galibi na ƙasashen Yankin Gabas ta Tsakiya.

An ba da rahoton cewar aƙalla 'yan ci rani guda goma suka mutu yayin da aka ceto wasu 135 a daran jiya alhamis zuwa yau Jumma'a.Bayan da jirgin ruwa marasa inganci da suke cikinsa ya kife a gabar tsibirin Kalymnos na Girka.

Jirgin ruwan wanda ya taso daga Turkiya wanda kuma ke kan hanyarsa ta zuwa Girka na ɗauke da 'yan cirani galibi na ƙasashen Yankin Gabas ta Tsakiya.Yanzu haka dai jami'an 'yan sanda na Girka na ci gaba da yin lalabe a cikin ruwan tsibirin ko da za su samu wasu sauran gawarwakin.Wannan hatsari dai ya zo ne kwanaki biyu kawai bayan nutsewar da wani jirgin ruwan ya yi da 'yan ci ranin a tsibirin Lesbos ya kashe mutane 17 a ciki har da yara 11.