Wani hari ya hallaka mutane 70 a Syriya | Labarai | DW | 31.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Wani hari ya hallaka mutane 70 a Syriya

Yara na daga cikin wadanda suka rasa rayukansu a wani mummunan harin da jiragen yakin Syriya suka kai kan wata kasuwa da ke Gabashin Damascus babban birnin kasar.

Akalla mutane 70 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu 550 suka samu raunuka a ranar jiya Jumma'a a wani hari da jiragen yakin kasar siriya suka kai kan wata kasuwa da ke birnin Duma a Gabashin Damas babban birnin kasar Siriya a cewar kungiyar Médecins sans Frontières (MSF) .

Hukumar kula da kare hakin bil dan Adam ta OSDH ta kiyasta mutane 59 da suka rasu sakamakon harin cikinsu har da yara kanana biyar sakamakon wata roka da aka harba da kuma harbi ta jiragen yakin kasar ta Siriya.

A cewar daraktan babban asibitin yankin mai samun tallafi daga kungiyar ta Médecins sans Frontières, wannan hari ya yi muni sosai, domin mutane na dauke da manyan raunuka abun da ta kai ga yanke sassan jikin mutane da dama a cewar wata sanarwa da kungiyar ta likitocin duniya ta Médecins sans Frontières ta fitar a yau Asabar.