1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wani dan gudun hijira ya sha duka a Jamus

Gazali Abdou Tasawa
August 30, 2018

A kasar Jamus wasu masu kyamar baki sun yi wa wani dan gudun hijira duka da ruwan ashar irin na nuna kyama a birnin Mecklembourg-Pomeranie na gabar tekun Baltika.

https://p.dw.com/p/341XJ
Deutschland Kontrolle von Flüchtlingen in Güterzüge
Hoto: picture-alliance/picturedesk.com/R. Mühlanger

Hukumar 'yan sanda ta birnin Mechlemburg-Pomeranie ta Gabas ta ce wasu mutane ne su uku suka tare dan gudun hijirar mai shekaru 20 a kan hanyarsa ta zuwa gidansa inda bayan sun yi masa ruwan ashar, biyunsu suka fada shi da duka da hannu a huska a yayin da na ukkunsu ya doke shi da kaca a baya. 

Bayan sun kaishi kasa sun kuma ci gaba da dukanshi inda suka karya masa karan hanci da farfasa masa jiki kafin daga bisani ya kwaci kansa ya kuma tsere da gudu. Hukumar 'yan sandar ta sanar da bude bincike kan wannan lamari.

 Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ta Jamus ke a baya-bayan nan fuskantar tarzoma ta masu akidar kyamar baki a birnin Chemnitz a jihar Saxony.