Wani dan al Shabaab ya mika kansa ga Somaliya | Labarai | DW | 27.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Wani dan al Shabaab ya mika kansa ga Somaliya

Daya daga cikin shugabannin al Shabaab ya mika kansa ga hukumomin Somaliya.

Wani fitaccen mayakin kungiyar al-Shabaab da ke kula da harkokin leken asiri ya mika kansa ga gwamnatin Somaliya da kuma rundunar kiyaye zaman lafiya ta Afirka ba tare da zato ko tsammani ba. Zakariya Ismail Ahmed Hersi na daya daga cikin shugabannin wannan kungiyar da Amirka ta yi alkawarin bayar da ladar kudi har miliyan uku na Dollar ga duk wanda ya samar da bayyanai kan inda suke boye.

Wannan mika kan dai ya biyo bayan rarrabuwar kawunan da ake fuskanta a kungiyar al-Shabaab da ke gaggwarmaya da makamai a Somaliya. Sai dai kuma ba a san ko har yanzu Zakariya Ismail na ci gaba da dasawa da kungiyar da ke da tsaurin ra'ayyin addini ko kuma ya raba gari da ita ba.

Ya zuwa yanzu dai kungiyar ta al-shabaab ba ta ce uffan ba game da mika kanshi da daya daga cikin shugabanninta ya yi. Da ma dai a baya-bayannan ta yi ta dibar kashinta a hannun sojojin gwamnati Somaliya da kuma rundunar Amisom ta kasashen Afirka.