Wani abu ya fashe a cikin wata mahaƙa a Ukraine | Labarai | DW | 04.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Wani abu ya fashe a cikin wata mahaƙa a Ukraine

Mutane 33 suka mutu a cikin wata mahaƙar kwal a gabashin Ukraine, bayan da wata gangar iskan gas ta fashe.

A gabashin Ukraine ana ci gaba da yin tababa a kan makomar wasu ma'aikatan haƙo ma'adinan kwal.Wadanda tun da farko kakakin majalisar dokokin ƙasar Volodymyr Groissaman ya ce illahirin ma'aikatan na mahaƙar da ke a gabashin ƙasar sun mutu a cikin haɗarin.

Kafin daga bisa ya sake dawowa a kan maganar da ya yi cewar har yanzu a a da masaniya a kan makomar mutane.