Wani ɗan ƙasar Amirka na uku ya kamu da Ebola | Labarai | DW | 09.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Wani ɗan ƙasar Amirka na uku ya kamu da Ebola

Jami'an kiwon lafiya na ƙasar sun ce mutumin ya kamu da cutar ne daga Saliyio.

Yanzu haka an isa da mutumin a wani asibitin da ke kusa da Atlanta inda ake yi masa magani. Wato asibitin da aka yi wa wasu sauran Amirkawan magani waɗanda suka kamu da cutar ta Ebola.

Wannan sanarwa na zuwa ne a daidai lokacin da Ƙungiyar lafiya ta duniya WHO ta ce sama da mutane dubu biyu suka mutu da cutar tun lokacin da anobar ta ɓarke. Hukumar ta kuma ce kusan rabi na waɗanda suka mutun sun cikka ne a cikin kwanaki 21 na baya-baya nan.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Pinado Abdu Waba