Wani ɗan Najeriya zai fiskanci shari'a a Amirka
August 28, 2013A Najeria wata kotu ta amince, da tisa ƙeyar wani ɗan ƙasar zuwa ƙasar Amirka don ya fiskanci shari'a. A farkon wannan watan ne ofishin jakadancin Amirka a Najeriya ya buƙaci da a tura musu ɗan Najeriya Lawal Olaniyi Babafemi, wanda ake zargi da aikata ta'addanci ya je ƙasar Amirka don a yi masa shari'a. Wasu takardun da aka fitar sun bayyana cewar, Babafemi da kansa ya amsawa jami'an binciken mayan laifuka na Tarayayar Amirka wato FBI, cewa ya ziyarci ƙungiyar Alƙa'ida a ƙasar Yamen, inda suka bashi kuɗi har dalar Amirka 8600, don ya koma Najeriya ya ɗauko musu sabbin mayaƙa, da ke iya yin magana da harshen ingilishi. Alƙalin da ya jagoranci zaman kotun a Abuja Ahmed Muhammed, ya ba da umarnin a tisa ƙeyar Babafemi don ya je Amirka ya fiskanci shari'a. Shi ma dai Babafemi wanda ake tuhumar da kasancewa dan ƙunkiyar Alƙa'ida, bai nuna rashin amincewar da hukunci ba.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Abdurahmane Hassane