Muna amfani da "Cookies" domin inganta abubuwan da muke wallafawa a intanet. Za ku iya samun karin bayani a kundin kare bayananmu.
Hukumar zaben Nijar ta ce ta shirya kaucewa kurakuran zabe da aka fuskanta a zagaye na farko na zaben shugan kasa
Hukumar zaben Nijar,CENI, ta gana da jam'iyyun kasar, inda ta bayyana musu sharuda da ka'idojin rajistar masu zabe da za ta fara yi wa 'yan kasar da ke ketare.
Hukumar Zabe mai Zaman Kanta a Jamhuriyar Nijar wato CENI, ta tattauna da 'yan jarida da ma kungiyoyin fararan hula domin bayar da bayani kan halin da ake ciki dangane da shirin kidayar 'yan Nijar da ke kasashen waje.
A wani yunkuri na zaben cike gurbi na majalisar dokoki, hukumar zaben Nijar ta fitar da jadawalin rijistar sunayen masu kada kuri'a daga kasashen ketare.
Hukumar Zabe mai Zaman Kanta a Jamhuriyar Nijar CENI tare da Hukumar Raya Kasashe ta Majalisar Dinkin Duniya PNUDD, sun shirya bita kan zabukan kasar da suka gabata.