Walwalar mata a Saudiyya na karuwa | Zamantakewa | DW | 02.09.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Walwalar mata a Saudiyya na karuwa

Shirin Abu Namu na wannan mako ya duba yadda mata da sauran al'ummar Saudiyya suka karbi dokar da ta bai wa matan kasar fita ba tare da rakiyar muharraminsu ba. 

Mahukuntan na Saudiyya dai sun amince da wasu sabin dokoki ne da ke bai wa matan karin 'yanci, ciki har'da ba su damar yin fasfo da yin  bulaguro su kadai ba tare da muharraminsu ba. Haka kuma sabuwar dokar ta bai wa matan damar sanar da auransu da kuma damar karbar takardar sakinsu kai tsaye daga kotu, ba sai ta hannun mahaifi ko maharraminsu ba.

Sauti da bidiyo akan labarin