1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wakilin MDD a Siriya zai gana da jami'an Amirka da Rasha

Mohammad Nasiru AwalJuly 25, 2016

A wani mataki na farfado da shirin tsagaita wuta a Siriya, za a gana tsakanin tsakanin manyan jami'an duniya a birnin Geneva.

https://p.dw.com/p/1JVjt
Österreich Wien Syrien Friedensgespräche - Staffan de Mistura
Staffan de Mistura lokacin wani taro a birnin ViennaHoto: Reuters/L. Foeger

A ranar Talatar nan wakilin Majalisar Dinkin Duniya a Siriya Staffan de Mistura zai tattauna da manyan jami'an kasashen Amirka da Rasha a birnin Geneva a wani matakin farfado da shirin zaman lafiya. Mai magana da yawun de Mistura, Jessy Chahine wadda ta tabbatar da wannan labarin, ba ta yi karin bayani ba game da ajandar taron ba, amma wakilin na Majalisar Dinkin Duniya ya sha kokarin ceto shirin zaman lafiya da ake fargaba ya ruguje gaba daya. A farkon wannan wata sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry da takwaransa na Rasha Sergei Lavrov sun ba da sanarwar cimma wata yarjejeniya kan abinda suka kira kwararan matakan farfado da shirin tsagaita wuta a Siriya a matsayin muhimmin mataki kafin sake komawa kan teburin shawarwari.