Wakilan kasashe sun kauracewa bikin rantsar da Yoweri Museveni | Labarai | DW | 13.05.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Wakilan kasashe sun kauracewa bikin rantsar da Yoweri Museveni

Wakilan kasashen Amirka da Kanada dana EU sun fice daga bikin rantsar da shugaban kasar Yuganda Yoweri Museveni a ranar Alhamis din nan, a wani yunkurin yin adawa da kalaman shugaban.

Wannan matakin da suka dauka ya zo ne jim kadan da bayyanar shugaban kasar Sudan Omar Hassan al-Bashir da hukumar ICC take nema ruwa jallo a bisa take hakkokin bil adama a yayin bikin rantsar shugaban Yoweri Musevenin.

Tun dai a yayin jawabin sa a gaban dubban wadanda suka hallara a bikin rantsar dashi shugaba Yoweri Museveni yayi shagube ga hukumar ta ICC wacce ya bayyana a matsayin hukumar da ke kunshe wasu mutane da basu da alkibla.

To sai dai a ta cewar mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Amirkan Elizabeth Trudeau, tawagar Amirka gami da wakilan Kungiyar Tarayyar Turai da kasar Kanada sun kauracewa bikin ne domin yin adawa da kalaman shugaba Yoweri Museveni.