1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyon da za su wakilci Jamus a kakar badi

Gazali Abdou Tasawa
May 16, 2018

Kungiyoyin Bayern Munich da Schalke 04 da Hoffenheim da kuma Dortmund ne za su wakilci kasar ta Jamus a gasar cin kofin zakarun Turai ta Champions Lig ta kakar badi

https://p.dw.com/p/2xoRn
Deutschland FC Bayern München v FC Schalke 04 - Bundesliga
Hoto: imago/ActionPictures/P. Schatz

A yayin da Kungiyoyin Bayer Leverkusen da Leipzig suka samu tikitin buga kai tsaye gasar cin kofin hukumar kwallon kafa ta Turai ta UEFA wato Europa Lig. Akwai sauran tikiti daya na shiga gasar Europa Lig bayan buga wasan ketara siradi na Play off  wanda kungiyar za ta koma ko dai a hannun Stuttgart da ke a matsayin ta bakwai ko kuma Frankfurt ta takwas idan har ta lashe kofin kasar Jamus a wasan da za ta buga da Bayern Munich a ranar Asabar.