1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wakilan DW a ƙasashen Afirka masu arziki

February 7, 2013

Bayan ƙasashen Asiya masu samun bunƙasa, ƙasashen Afirka sun yunƙuro musamman saboda albarkatun ƙarƙashin ƙasa. Sai dai a wurare da dama ana fama da talauci.

https://p.dw.com/p/17aGX
Hoto: DW/Bob Barry

Ma'adinan ƙarƙashin ƙasa a Afirka kamar tagulla, ƙarafa da duwatsu masu daraja kamar zinariya da lu'ulu'u, man fetir da iskar gas suna taimakawa wajen bunƙasa tattalin arzikin ƙasashen Afirka da dama. Wasu ƙasashen kamar Angola mai arzikin man fetir tana samun bunƙasar tattalin arziki kimanin kashi 20 cikin 100 a shekara. Mozambi kuwa ga misali tana kan kyakkyawar hanyar samar wa duniya kwal da iskar gas. Nahiyar Afirka na samun bunƙasa yayin da tattalin arikin duniya ke fuskantar ƙarancin albarkatun ƙarƙashin ƙasa.

A lokaci ɗaya bunƙasar albarkatun ƙarƙashin ƙasar na zama wani abin rashin tabbas ga tsarin tattalin arzikin Afirka, kasancewa sun dogara ne ga kasuwannin duniya da rashin daidaiton farashi da bukatun ƙasashe. Gurbatar muhalli, almundahana da rikice rikice masu nasaba da rabon albarkun ƙasa na zaman wani naƙasu ga wannan arziki. Shin me ya saura na wannan arziki ga ƙasashen Afirka da kuma al'ummomin wannan nahiya? Wakilan DW sun bi diddigi don gano amsar wannan tambaya.

Infografik: Wichtige Rohstoff-Exporteure in Afrika HAU Hausa

Mawallafa: Julia Hahn / Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu