Wakilai suna canza sheka a majalisun Najeriya | Siyasa | DW | 19.12.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Wakilai suna canza sheka a majalisun Najeriya

Jam'iyar PDP ta fara korafi da shirin zuwa kotu, bayan da wasu wakilanta a majalisun dokokin Najeriya suka fara canza sheka zuwa babbar jam'iyar adawa ta APC

Yan siyasa da sauran masana na ci gaba da martini dangane da sauyin sheka da wasu 'yan majalisun Tarayyar Najeriya suka yin a barin jamiyyar PDP mai mulki zuwa jam'iyyar 'yan hamayya ta APC, wannan sauyin sheka dai wasu na ganin babbar barazana ce ga jamiyyar PDP mai mulki wacce ita kuma ke hankoron daukar mataki akan wadannan masu sauyin sheka.

Bayan gwamnonin PDP da suka yi wa jam'iyyar tutsu karshe suka fice daga cikin ta yanzu haka yan majalisun wakilai 37 ne suka tattara yanasu-yanasu suka kuma bi bayan wadannan gwanoni in da suma suka ce in dai batun PDP ne sun yada kwallon mangwaro domin hutawa da kuda, lamarin da masu fashin baki a harkar siyasa ke cewa wannan wani ci gaba ne ga siyasar Najeriya matukar jakar "Ghana must go" bata sauyawa yan majalisar tunani ba. Dr Saidu Ahmad Dukawa, malami ne a sashin kimiyyar siyasa a jamiar Bayero ta Kano. Yace wannan mataki tamkar juyin juya hali ne ga jam'iyyar PDP mai mulki musamman la'akari da yadda matakan suka rinka faruwa bi da bi.

Sai dai kuma wani dattijo mai fashin baki kan al amuran yau da kullaum, Alhaji Aliyu Sumaila na ganin cewar wannan sauyin sheka yaudara ce, sai dai fa idan an dora shi akan gwadaben da ya dace. Shima a nasa bangaren Umar Sa'idu Tudun Wada, gogaggen dan jarida na ganin cewar wannan al'amari tamkar wata 'yar manuniya ce da ka iya nuna balagar siyasar Najeriya duba da cewar a baya yan wasu jam'iyun sun yi irin wannan hijira zuwa jamiyyar PDP ba tare da daukar wani mataki akansu ba. Zuwa yanzu dai wannan batu shine babban abin da yanzama maudu'in tattaunawa, sai dai abin jira a gani shine irin matakin da jam'iyyar PDP zata dauka, musamman ganin tana hankoran tafiya kotu.

Mawallafi: Nasiru Salisu Zango
Edita: Umaaru Aliyu

Sauti da bidiyo akan labarin