Wajibcin tattaunawa a rikicin Sudan biyu | Siyasa | DW | 14.02.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Wajibcin tattaunawa a rikicin Sudan biyu

A Ranar juma'a wa'adin da AU ta dibarwa gwamnatin Sudan na komawa kan teburin sulhu da takwararta ta Kudu da kuma 'yan tawaye game da rikicin kordofan ta kudu ke cika.

Mutane dubu 65 ne suka kaurace wa matsaugunansu a wannan yanki tun bayan da sojojin Sudan da kuma 'yan tawaye da ke neman ballewa suka fara ba wa hammata iska a kudancin Kordofan da kuma kusa da tekun Nilu.Farmakin da sojojin saman Sudan suka kai a Kordofan ta kudu a farkon watan febrerun 2013 ya dauki hankali kafofin watsa labarai na kasashen Afirka. Ba don komai ba, sai don asarar da ya haddasa ciki kuwa har da ragargaza ginin wata makaranta da ya yi. Daidai da Kungiyoyin da ke kare hakkin bil Adama sai da suka yi Allah wadarai da matakin soje da fadar mulki ta khartum ke dauka a wannan yanki, suna ma su danganta shi da "kisar kare dangi". Raphael Veicht na kungiyar agaji ta Jamus mai suna "Anamur", ya shafe shekaru hudu ya na aikinjin a kudancin Kordofan da kuma kewaye. Ya tabbatar da hare-haren da sojojin Sudan suka saba aiwatar akan walau takwarorinsu na Sudan ta Kudu ko kuma 'yan tawayen SPLM.

Afrika Südsudan Südkordofan Flüchtlinge

Duban mutane sun kauracewa matsugunansu a kordofan ta Kudu

"Sojojin Sudan da Sudan ta kudu na yunkurin mamaye wannan yankin domin mayarwa karkashin ikonsu. Wannan ne ke haifar da hare-hare ta sama kusan a kullum. A yanzu haka da muke cikin kaka suna kai hare-haren ne ta kasa ."

Dalilan tayar da kayar baya a jihohin Kordofan da Nilu

Jihohin Kordofan ta Kudu da kuma ta kogin Nilu na kan iyakar Sudan ta Arewa ne da kuma Sudan ta kudu wacce ta samu 'yancin kanta a watan Yulin 2011. Babban burin da aka sa a gaba a halin yanzu shi ne shirya zaben raba gardama, da nufin bai wa 'yayan wannan yanki damar zaban inda suke so su kasance. Erst Jan na kungiyar International Crisis Grup ya ce rashin bai wa 'yayan wannan yankin dama ne, ya sa su tayar da zaune tsaye.

"Bayan samun 'yancin kai da Sudan ta kudu ta yi, 'yan Kordofan ta kudu ba su samu damar kada ta su kuri'ar raba gardama ba. Yankin na ci gaba da zama wani bangare na kasar Sudan. Sai dai kuma wasu mazauna wannan yanki na adawa da haka. Saboda haka ne suka fara tayar da kayar baya."

Rikicin na Sudan na da nasaba da kabilanci

Jihohin biyu na Kordofan ta Kudu da kuma ta Nilu sun kunshi mutane miliyan uku da dubu dari biyar, galibinsu bakaken fata kuma kiristoci da kuma mabiya addinan gargajiya. Yayin da a Arewacin kasar, akasarin jama'a musulmi ne kuma suna da dangantaka ta jini da larabawa. Jehanne Henry da ke shugabatar reshen Afirka na kungiyar Human Right Watch, cewa ya yi wannan rikici an Sudan ya kabilanci ne.

"Akwai matakai na cin zarafi da kabilanci da ake nunawa gwamnatin Sudan ta Kudu. A watannin da suka gabata, shugaban kasa cikin wani jawabinsa ya danganta mazauna kogin Nilu da kananan kwari da ya kamata a kawar."

Südsudan USA Außenministerin Hillary Clinton bei Präsident Salva Kiir in Juba

Amurka ta tsoma baki a rikicin Sudan da Sudan ta Kudu

Kungiyar Gamayyar Afirka da kuma kasar Amurka sun nemi gwamnatin Sudan ta tattauna da wadanda suke neman ballewa da kuma gwamnatin Sudan ta Kudu. Kwararrun sun nunar da cewa Jihohin na Kordofan da kuma ta Nilu sun kunshi dimbin albarkatun man fetur. Tun watan Afrilun shekara ta 2012 ne, rikici ya barke tsakanin kasashen Sudan da Sudan ta kudu game da wannan yanki. A halin yanzu dai mutane dubu 700 ne ke fama da karancin abinci a jihohin biyu da rikicin ya shafa. Kungiyoyin da suka himmatu wajen bayar da agaji a Kordafan ta kudu da kuma Nilu na cin karo da matsaloli iri daban daban.

Rahoto cikin sauti na kasa

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Mohammad Nasiru Awal

Sauti da bidiyo akan labarin