Wai shin ya tsarin zaben Jamus yake? | Jigo | DW | 04.09.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Jigo

Wai shin ya tsarin zaben Jamus yake?

Shin wane ne zai lashe zabe tsakanin Merkel da Steinbrück? Duk da cewa Jamusawa za su iya kada ma wani dan takara kuri'a, amma jam'iyya ce ta fi muhimmanci a zaben kasar.

"Duk dan takara da bai tsaya karkashin inuwar wata jam'iya ba, sa'a rageggiya ya ke da ita ta samun kujerar dan majalisa da kuma zama daya daga cikin mambabi 600 da ta kunsa." Da wadannan kalamai ne daya daga cikin jiga-jigan 'yan majalisar Bundestag ta yi ma wata matashiya bayani, lokacin da ta tabbayeta yadda aka yi a samu kujerara a majalisa.

Duk wani dan takara mai zaman kansa da wata jam'iyar siyasa ba ta tsayar da shi ba ya na bukatar tarin goyon baya. Kundin tsarin mulkin kasar ta Jamus ya bayyana cewar "Jam'iyun siyasa ne ke bayar da gudunmawa wajen tafiyar da al'amuran kasa." Sai dai kuma masana harkokin siyasa sun nunar da cewar inda gizo ke saka shi ne jam'iyun ne za su iya tantance wanda zai iya yin siyasa. Wannan ko ya na kunshe cikin tsarin zabe na Jamus mai ruwa biyu.

Jamusawa da ke da shekaru akalla 18 a duniya ne suka cancanci kada kuri'a. Yawansu a yanzu ya kai miliyan 61,8 ciki har da mutane miliyan uku da za su kada kuri'a a karon farko. Hukumar kidaya ta kasa wacce shugabanta ke shirya zabe ne ta bayar da wadannan alkaluma.

Shugaban hukumar da ke kula da zabe ne ya cancani wallafa sunayen daukacin 'yan takara da za su fafata tsakaninsu. Ba shi da izinin watsi da takara matikar ba ta take kundin tsarin mulki ko kuma ta na barazanar ga demokaradiya ko kuma zaman lafiya ba. A ranar 22 ga watan satumba jam'iyu 34 ne za su kalubalanci junansu. Sai dai a halin yanzu shida daga cikinsu ne ke da wakilci a majalisa ta Bundestag: CDU da CSU, SPD, FDP, masu rajin kare muhalli da kuma Die Linke.

Dokokin zaben Jamus sun shekaru 60 suna tasiri

Baya ga manyan jam'iyun siyasa, kanana ma na iya samun kujeru a majalisa. Sai dai bisa ga dalilai na demokardiya kananan jam'iyun na iya kulla kawance tsakaninsu don samun karfin fada a ji. Wadanda suka dora Tarayyar Jamus a kan tubalin da ta ke yanzu haka, sun dauki mataki da suka wajaba domin hanata fadawa cikin rikici, kamar yadda ya so ya faru a shekarun 1920. Sun tsayar da shawarar cewa jam'iyun da suka lashe fiye da 5% za su iya shida cikin majalisa.

Aufteilung der Sitze im Bundestag, Deutscher Bundestag, Mehrheitswahl, Direktkandidaten,Erststimme, Zweitstimme,Verhältniswahlsystem,Wahlkreise

Tsarin zabe a Jamus

Ba a so jam'iyu su ci karansu ba tare da babbaka ta hanyar fitar da gwanayensu kai tsaye ba. 'Yan kasa aka ba wa wuka da namar zaban wanda suka ga ya dace. Burin da aka sa a gaba dai shi ne kusanci juna tsakanin 'yan siyasa da kuma 'yan kasa. A Jamus dai a mazabu 299 'yan takara ne ke tallata kansu da kuma manufofinsu. Bisa ga tsarin zaben wannan kasa zagaye biyu na zabe ake da su. Tsarin bai canja ba a cikin shekaru 60 da suka gabata.

Zaben Tarayyar Jamus na da ruwa biyu

Kowane bajamushe na kada kuri'a biyu. Kuri'arsa ta farko ta zamban dan takaran wata jam'iya da ya ke ganin cewar zai iya kare muradunsa idan ya samu kujara a majalisa. Dan takara da ya samu mafi yawan kuri'u ne ke lashe zabe a kowace mazaba.

Wahlhelfer, Auszählung der Stimmen läuft

Kuri'a ta biyu ce ta fi muhimmanci domin da ita ake zaban jam'iyar siyasa. Yawan kuri'un da kowace jam'iya ke samu ne ke tantance kason da za ta samu a majalisar dokoki da ma dai 'yan majalisa da za su yi jiran gado. Ba a damawa da duk jam'iyun da suka samu kasa da kashi 5% na kuri'un da aka kada.

Tsarin zaben Jamus ya yi ta shan suka a karo da dama a tsawo rayuwarsa. Babban dalilin da aka bayar shi ne sabanin demokaradiya rabi 'yan majalisa al'uma ke da ikon zaba kai tsaye.

Mawallafi: Dick Wolfgang
Edita: Mouhamadou Awal