Wahalolin dalibai makafi a Tahoua | Zamantakewa | DW | 16.01.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Wahalolin dalibai makafi a Tahoua

Rashin kayan aiki da suka dace, yana haddasa cikas a matakan ilmantar da dalibai makafi a makarantun jamhuriyar Nijar

A birnin Tahoua na Jamahuriyar Nijar, dalibai makafi yan makarantar
sakandare na kokawa da halin da suke ciki na karbar darasi,inda suke
fatan samun cikokun kayan aikin da zasu basu damar samun ilimin da
suke kwadayin samu maimakon suyi bara.

Bayan makarantun Piramare da aka kafa na makafi, a nan Jihar Tahoua
duk dalibin da ya samu Certificate na karshen Piramare ya kan shiga
sakandare inda a nan Tahoua makarantar CEG ta daya ce ke karbar
wadannan makafi, inda suke karatu tare da sauran dalibai masu gani.
Saidai yayin da da dama ke ganin kokarin wadannan matasa na neman
ilimi maimakon suyi bara, su kansu makafin sun gano cewa tafiyar na da
sarkakiya, sabili da rashin kayan aiki irin nasu, inda hakan ke
haifar musu da cikas wajan daukan darasi. Halilu Issa dalibi ne makaho
dan makarantar sakandre. Yace:


"Wannan abu da kake gani mai dan tsinke shine muke sawa muna
rubutu dashi, to da zaran ka samu minti talatin zuwa awa guda, to sai
kusan hannun mutun ya ja ruwa saboda babu dadin aiki, dan haka idan da hali to a sama mana kayan aiki kamar na'ura ta rubutu."

Daga nashi bengare Mamane Sani shima wani dalibin makaho jaddada
matsalolin nasu yayi:

"Kayan aiki gaskiya bamu da su domin idan da mashin muke
rubutu, abun da zamuyi tsawon awa guda to zamuyi shi cikin minti
talatin idan muka samu na'urar rubutu."

Sanin kowa ne a nan Jamahuriyar Nijar da ma sauran kasashe da
dama cewa makanta ko nakasa ba wani abu ne dake hana neman ilimi ba,
inda ma ake samun wadanda ke zama abun koyi cikin su, amma dai hakan na faruwa ne tare da manya manyan kalubane.Nafissa Mamane ita ma daliba ce da bata gani ta tabo batun matsalar zuwa makarantar kanshi. Tace :

"Wani bi muna daukan wajan minti talatin bisa hanyar ga motoci
ga mashin mashin idan da zamu samu masu taimaka mana fannin ma daukan hayar kabu-kabu ko taxi don mu samu sauki domin muna nesa kuma wasu basu da halin daukar abun hawa tunda muna son karatu, kuma muna son yaki da yawon bara domin bara na haifar da talauci ne."

Oberschüler in Tahoua, Niger

Daliban Sakandare a birnin Tahoua na jamhuriyar Nijar

A cewar darektar makarantar CEG ta daya ta nan Tahoua, Umaru Danladi,
inda wadannan makafi suke, makanta dai, ko ma ace nakasa, ba wani gazawa ba ce domin su kansu maluman wannan makaranta sun tabbatar da cewa su wadanda basa ganin sunfi ma masu ganin ilimi da saurin fahimtar darussa.


"Lalle suna son samun kaya na zamani na rubutu, dan jin dadin
daukar darasi cikin aji, kuma muna ganin sunfi ma masu idanun fahimta
domin maluman su da kan su ke fadar cewa suna da hazaka sosai, dan
haka muna fata da a taimaka musu dan suma su zan wani abu kamar kowa."

Daga bisani darekta Umaru Danladi na makarantar Collegi ta daya a nan
Tahoua kira yayi ga sauran dalibai da su rinka kula wajan taimakawa
wa'innan abokai nasu ko da sun gane su ne bisa hanya ko a nan cikin
makaranta domin muddin dai mutun na da rai to ba'a gama halittar sa ba
ma'ana nakasu na iya samun kowa.

Mawallafi: Salissou Boukari

Edita: Umaru Aliyu