1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wadanda suka mutu a Indonesiya sun karu

December 24, 2018

Alkaluman wadanda suka salwanta a ibtila'in guguwar tsunami da ta afka wa kasar Indonesiya sun kai mutum 280. Akwai kuma daruruwa da suka jikkata.

https://p.dw.com/p/3Aa9u
Indonesien Nach dem Tsunami
Hoto: Reuters/Antara Foto

Hukumar da ke kokarin kare afkuwar bala'o'i a Indonesiya wadda ta sanar da alkaluman, ta ce baya ga wadanda suka mutu, wasu sama da mutum dubu guda ma sun jikkata.

Akwai wasu mutum 57 da har yanzu ba a san inda suka shiga ba, kuma da yiwuwar wadanda suka mutu ya karu matuka.

Ya zuwa yanzu hukumomin Indonesiyar sun tabbatar da cewa sama da mutum dubu 11 da 600 ne bala'in ya raba da muhalli.

Bala'in ya kuma afka wa mazauna yankunan Java da Sumatra ne, bak tatan da yammacin ranar Asabar da ta gabata.

Haka nan kuma matsalar ta watsu i zuwa ga wasu gundumomin kasar akalla biyar ya zuwa halin da ake ciki.