Wace kasa ce ke da karfin lashe kofin AFCON a 2024?
January 12, 2024Afcon ta kasancewa tsohuwar gasar kwallon kafa da karon farko ya gudana shekaru 67 da suka gabata, kuma har yanzu gasar cin kofin nahiyar Afirka na daya daga wadanda babu tabbas game da wanda zai iya ganin badi. Hasali ma dai, a gasanni 37 da aka shirya, kasashe 15 ne suka yi nasarar daukar kofin, inda kusan giwayen nahiyar suka taba lashewa akalla sau daya cikin tarihinsu. Amma wasu kananan kasashen kwallon kafa ma sun samu damar cire wa kansu kitse a wuta, kamar yadda ya faru da Zambiya da ta lashe kofin a 2012.
A shekarun baya-bayan nan, manyan kungiyoyi kamar Aljeriya ko Senegal ne suka taka rawar gani, amma tarihi ya nuna cewa komai na iya faruwa a lokacin Afcon. Ba a sanya Côte d' Ivoire a rukunin wadanda za su iya zuwa a matsayin farko ba duk da bakuncin gasar da ta dauka. Dama ba kasafai ake samun kungiya da take nasarar buga wasan karshe a gaban jama'arta a gasar Afcon. Tawagar karshe da ta dauki kofin nahiyar a gida ita ce Masar a 2006. Kuma duk da cewar Côte d'Ivoire ta nuna bajinta a wasannin sada zumunta, amma tawagar ba ta yi wasannin tankade da rairaya domin samun damar cancanta ba saboda ita ce ke daukar bakunci.
Senegal na ci gaba da daukar hankalin masharhanta
Amma a daya hannun, Senegal da ke rike da kofin Afirka na daya daga cikin kasashen da ake ganin za su iya taka rawar gani, ko da shi ke tauraron kwallon kafar kasar Sadio Mane ya ce ba za a iya sannin maci tuwa ba, la'akari da cewar "gasar za ta kasance daya daga cikin mafi tsauri tun lokacin da aka fara Afcon" saboda burin da kasashe ke da shi.
Amma Ibrahima Traore, tsohon dan wasan Bundesliga na Jamus kuma tsohon kyaftin na tawagar kasar Guinea ya ce akwai bukatar sa ido a kan Senegal. Ya ce: "Watakila Senegal ba ta da wani abin burgewa a fagen kwallon kafa sabanin sauran, amma kungiya ce da ta saba yin nisa a gasa, da yin abin da ya dace don tsallakewa zuwa zagaye na gaba ko ma zuwa wasan karshe, ko ma lashe gasa. Wannan na dan tuna min kasar Faransa, wacce ba ta taka rawar gani a gasa amma a koda yaushe take iya cimma burinta."
Maroko ko Najeriya: wa zai iya ganin badi?
Maroko da ta fito daga yankin Maghreb za ta so nuna cewa ita ba kanwar lasa ba ce sakamakon bajintar da ta nuna a gasar cin kofin duniya ta FIFA ta 2022, inda ta zo ta hudu. Sannan Masar za ta iya dogaro kan 'yan wasa masu inganci da suka fito daga manyan kungiyoyi kamar Al Ahly da Zamalek, kuma ta yi kokarin kawo Mohamed Salah a karon farko wajen kai labari. A nata bangaren Aljeriya wacce ta lashe AFCON a 2019, za ta yi kokarin wanke abin kunya na rashin tabuka abin kirki a Kamaru a 2021.
Najeriya wacce rabon ta kai bantenta a gasar kwallon kafa ta nahiyar Afirka tun shekaru 11 na da kwararran hujjoji na mafarkin lashe kofi. Babban abin tinkahon Super Eagles shi ne Victor Osimhen wanda ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon Afrika a kwanakin baya. Sannan Super Eagles na da askarawan gaba na gani a fada irin su Boniface da Lookman da Chukweze da Iheanacho, amma ba zai wadatar wajen lashe irin wannan gasa mai muhimmanci ba. Ko da tsohon dan wasan Najeriya Jay Jay Okocha kuma tsohon dan wasan Eintracht Frankfurt sai da ya koka game da rashin samun daidaito a fannin nasarori.
Sauran kasashen da suke ganin cewar za su iya cimma burinsu a AFCON sun hada da Kamaru da Ghana da Mali da Guinea da Burkina Faso da Tunisiya. Amma Ibrahima Traore tsohon kyaftin na tawagar kasar Guinea ya ce komai na iya faruwa a gasar ta bana.
Traoré ya ce: "A kowace gasa akwai abubuwan ban mamaki, mun shaidar da haka a kan Gambiya a gasar karshe da aka buga, ko kuma Saliyo da ta yi kunnen doki da Aljeriya. Wannan ci-gaban ya samu ne saboda kara yawan kasashen da ke halartar Afcon da aka yi. Kungiyoyin na wasan ta kife a a filin kwallo don cimma wani buri na musamman. Don haka ina ganin za a sake samun wasu abubuwan ban mamaki a bana."
Kasancewar tana kasa tana dabo a wannan gasa, taurarin 'yan wasan kwallon kafa za su yi duk abin da zai taimaka wa tawagarsu cimma burinsu. Victor Osimhen na Najeriya da Mohamed Salah na Masar da Sadio Mane na Senegal da Mohammed Kudus na Ghana da Serhou Guirassy na Guinea suna taka leda a manyan lig naTurai da ma na duniya baki daya, kuma wasu na da gogewar lashe babbar gasa.