Wace ƙasa ce mafi ƙanƙanta a nahiyar Afirka | Amsoshin takardunku | DW | 11.05.2009
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Wace ƙasa ce mafi ƙanƙanta a nahiyar Afirka

Taƙaitaccev bayani game da ƙasar da ta fi kowacce ƙasa ƙanƙanta a nahiyar Afirka.

default

Shugaban ƙasar Gambiya AlHadji Yahya Jammeh

Tambaya: Tambaya ta farko a shirin namu ta fito daga hannun Malam Jibo Mansur Keffi daga jihar Nasarawa a tarayyar Najeriya. Ya ce sashen Hausa na Deutsche Welle, ina so ku sanar da ni ƙasar da ta fi kowacce ƙasa ƙanƙanta a nahiyar Afirka?

Amsa: Idan aka haɗa da tsibirai a matsayin ƙasashe da ke nahiyar Afirka, to ba ayi laifi ba idan aka ce tsibirin Seychelles ne yankin ƙasa mafi ƙanƙanta a Afirka mai faɗin murabba'in kilomita 453. Amma idan aka cire tsibirai a lissafin, to ƙasar Gambiya ce mafi ƙanƙantar ƙasa da ke da faɗin murabba'in kilomita 11,300 a faɗin nahiyar ta Afirka.

Jamhuriyar tsibirin Seychelles dai kamar yadda cikakken sunan yake haɗaka ce ta tsibirai 155 dake tekun Indiya mai nisan kilomita 1500 gabas da ainihin duƙulalliyar nahiyar Afirka. Kuma Jamhuriyar tsibirin na Seychelles ya kasance arewa maso gabas da tsibirin Madagaska.

Sauran maƙwabtan tsibirai da su ke maƙwabtaka da shi sun haɗar da na Zanzibar daga yamma, sai kuma na Mauritius da kuma Reunion daga kudu. Can kuwa daga kudu maso yamma akwai tsibiran Comoros da Mayotte. Haka kuma a arewa maso gabas akwai Suvadives ɗin Maldives. Wannan tsibiri dai na Seychelles, shi yake da mafi ƙanƙantar al'umma a faɗin ƙasashe da kuma yankunan tsibirai da ke nahiyar Afirka baki ɗaya.

Ita kuwa ƙasar Gambiya wadda ake kira jamhuriyar Gambiya, ita ce ƙasa mafi ƙanƙantar yawan al'umma a tsakanin ƙasashen da ke dunƙule cikin nahiyar Afirka, idan aka game lissafin tsibiran ƙasashe. Kuma ta yi iyaka da ƙasar Senegal daga arewa da gabas da kuma Kudancinta. Sannan ta yi iyaka da ƙaramin mashigin ruwan tekun Atlanta daga yamma.

Tsawon nisan iyakokin ta dai-dai yake da nisan tsawon kogin nan mai suna kogin Gambiya, wanda ya samo sunansa daga sunan ƙasar ta Gambiya. kuma ya kwaranya ta tsakiyar kasar zuwa cikin tekun Atlanta ɗin. A dai ranar 18 ga watan Fabarairu 1965, Gambia ta samu 'yancin kanta da hannun Ingila, tare kuma da shiga cikin ƙungiyar ƙasashe renon Ingila. Banjul dai shi ne fadar mulkin ƙasar, amma Serrekunda ne birni mafi girma da tarin al'umma a ƙasar.

Mawallafi: Abba Bashir

Edita: Ahmad Tijani Lawal