Wa′adin Ariel Sharon ya cika | Labarai | DW | 11.01.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Wa'adin Ariel Sharon ya cika

Bayan kwashe tsahon shekaru takwas a kwance ba tare da sanin inda kansa ya ke ba, tsohon Firaministan Isra'ila ya mutu.

Gidan radiyon sojojin kasar Isra'ila ya sanar da cewa tsohon Firaministan kasar Ariel Sharon, ya mutu bayan da ya kwashe tsahon shekaru 8 a cikin halin rai kwakwai mutu kwakwai. Ya mutu yana da shekaru 85 a duniya. Gidan Radiyon ya ruwaito cewa wani dan uwan marigayin ne ya sanar da mutuwar tasa.

Kawo yanzu dai asibitin Sheba da aka kai Sharon da kuma ya kwashe tsahon shekaru takwas yana sume basu ce komai kan mutuwar ta sa ba, sai dai kakakin asibitin ya ce za su bada wata sanarwa a nan gaba a wannan asabar (11.01.14) da misalin karfe uku agogon GMT.

Sharon dai ya tsinci kansa cikin shanyewar jiki sakamakon bugun zuciya da ya samu a ranar 4 ga watan Janairun shekara ta 2006, wanda hakan ya sanya ya shiga halin da bai san inda kansa ya ke ba inda jikin nasa ya tsananta a ranar daya ga wannan watan na Janairu bayan da ya samu matsalar koda sakamakon tiyatar da aka yi masa.

Tuni dai Firaministan kasar mai ci yanzu Benjamin Netanyahu ya bayyana alhininsa yana mai cewa Sharon din zai ci gaba da kasancewa a zukatan 'yan kasar ta Isra'ila.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Saleh Umar Saleh