von der Leyen ta zama shugabar EU | Siyasa | DW | 18.07.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

von der Leyen ta zama shugabar EU

A karon farko cikin tarihi Kungiyar Tarayyar Turai ta zabi mace a matsayin shugabar hukumar gudanarwa ta EU. Ministar tsaron Jamus Ursula von der Leyen ce ta yi nasarar hayewa kan wannan mukami.

An haifi Ursula von der Leyen kimanin shekaru sittin da suka gaba a birnin Brussels na kasar Beljiyam kuma ita da mahaifanta wadandan Jamusawa ne sun zauna a birnin na Brussels har lokacin da cika shekaru 13 da haihuwa. Ta fuskar ilimin boko dai von der Leyen karanci tattalin arziki kafin daga bisani ta sake komawa makaranta don yin karatun zama likita kuma bayan ta kammala shi ne ta fara harkoki na siyasa inda ta shiga jam'iyyar nan ta CDU a shekarar 1990.

Bayan shigarta harkokin siyasa sosai ta rike mukamai da dama ciki kuwa har da 'yar majalisar ta jiha a jihar nan ta Lower Saxony a shekarar 2003 kafin daga bisani kuma shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta nadata minista da ke kula harkokin iyali da lafiya sai kuma daga bisani ta kasance ministar harkokin tsaro wadda ita ce mace ta farko da aka nada kan wannan mukami kuma har yanzu tana rike da shi. Da dama na kallonta a matsayin wadda ta kawo sauye-sauye da dama ciki kuwa har da batun sake fasalta rundunar sojin Jamus da kuma kokari wajen amfani da sojin ruwanta kan batun 'yan gudun hijira.

Sauti da bidiyo akan labarin