Vladmir Putin ya soke wata ziyarar da ya shirya kai wa a Faransa | Labarai | DW | 11.10.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Vladmir Putin ya soke wata ziyarar da ya shirya kai wa a Faransa

Fadar gwamnatin Rasha Kremlin ta sanar da cewar shugaba Vladmir Putin ya soke ziyarar da ya shirya kai wa a Faransa nan gaba a makon gobe 19 ga wannan wata domin ganawa da takwaran aikinsa Francois Hollande.

Ziyarar ta Vladmir Putin wacce ba ta aiki ba ce, an dade da tsarata domin halartar wani bikin kaddamar da wata Cocin Orthodox ta Rashar a birnin Paris.Sai dai  masu aiko da rahotannin sun ce shugaban na Faransa yana yin dari-darin ganawa da shugaban na Rasha a Fadar Elysée,sakamakon zargin da ake yi wa  gwamnatin shugaba Bashar al Assad na Siriya da laifin aikata kisan kare dagin a Aleppo,tare da taimakon sojojin Rasha.Rikicin diflomasiya ya kara zafafa  tsakanin kasashen yammacin duniya da Rasha,tun bayan da Rashar ta hau kujera naki a kan kudirin MDD wanda Faransa ta gabatar na tsagaita wuta a yakin da ake yi a Aleppo.