Viktor Yanukovitch ya ce ba zai yi marabus ba | Labarai | DW | 22.02.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Viktor Yanukovitch ya ce ba zai yi marabus ba

Shugaba Viktor Yanukovitch na Yukren ya kamanta abin da ke faruwa a ƙasarsa da cewar wani yunƙurin juyin mulki ne.

Yanukovitch wanda yanzu haka yake a wani yankin gabashin ƙasar inda yake da rinjayen magoya baya a Kharkive kan iyaka da Rasha ya ce ba zai ajiye aikin ba. Ya ce:'' Ba zan yin marabus ba saboda ko ni zaɓaɓen sugaban ƙasa ne, sannan kuma ba zan ficce daga ƙasar ba.''

Shugaban ya yi alƙawarin yin duk abin da yakamata domin kaucewa zubar da jini. Tsakanin ranar Talata zuwa Alhamis mutane 80 aka kashe a birnin Kiev. A halin da ake ciki majalisar dokokin ƙasar ta Ukraine ta kaɗa ƙuri'ar tsige shugaban ƙasar, kana majalisar ta yanke shawarar gudanar da zaɓen sahugaban ƙasa na kafin wa'adi a ranar 25 ga watan Mayun da ke tafe.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe