Viktor Janukovitch ya miƙa wa ′yan adawa hannu | Labarai | DW | 11.12.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Viktor Janukovitch ya miƙa wa 'yan adawa hannu

Shugaban Yukren ya fara neman bakin zaren warware rikicin siyasar ƙasarsa cikin ruwan sanyi bayan da aka zargeshi da amfani da ƙarfi a kan 'yan adawa.

Shugaban ya yi kira ga 'yan adawan kasarsa da zama kan teburin tattaunawa domin gano bakin zare warware rikicin da ƙasar ke fama da shi. Wannan kuwa ya zo ne sa'o'i ƙalilan bayan da 'yan sanda suka yi amfani da ƙarfi wajen tarwatsa gangamin adawa da gwamnati a dandalin haɗin kai da ke Kiev kafin daga bisani su zuba musu ido.Wannan rikicin dai shi ne irinsa mafi tsauri da Yukren ta fuskanta tun bayan ƙaddamar da juyin juya hali a shekara ta 2004.

Makwanni biyu 'yan adawan na ƙasar suka shafe suna zanga-zangar lumana da nufin bayyana rashin jin daɗinsu da matakin da Janukovitch ya ɗauka na juya wa Ƙungiyar Gamayyar Turai baya. Sai dai kuma a yanzu gwamnatin ta buƙaci EU ta bata tallafin miliyan dubu 20 na Euro matiƙar ana so ta bayar da kai domin bori ya hau. Shugaba Janukovitch ya sha jadadda muhimmancin kyautata hulɗar cinikayya tsakanin ƙasarsa da Rasha.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Abdourahamane Hassane