Venezuwela: Mutane 37 sun mutu a boren gidan kaso | Labarai | DW | 17.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Venezuwela: Mutane 37 sun mutu a boren gidan kaso

Gwamnatin Venezuwela ta tabbatar da mutuwar mutane akalla 37  a yayin da wasu 18 suka ji rauni a cikin wani bore da ya barke a wani gidan kaso na jihar Amazonas ta Kudancin kasar. 

Gwamnatin Venezuwela ta tabbatar da mutuwar mutane akalla 37  a yayin da wasu 18 suka ji rauni a cikin wani bore da ya barke a wani gidan kaso na jihar Amazonas ta Kudancin kasar. 

Lamarin dai ya wakana ne a lokacin da jami'an tsaro na wata rundunar musamman ta ofishin ministan cikin gida da kuma shari'a suka yi kokarin kwantar da boren da 'yan kason suka tayar a gidan kason na birnin Puerto Ayacucho mai kunshe da 'yan akso 103. 

Mahukuntan shari'a na kasar sun sanar da nada wasu masu aikin bincike guda biyu domin gudanar da bincike kan mutuwar mutanen. Kuma gwamnan jihar ta Amazonas ya sanar da cewa a halin yanzu an dauke 61 daga cikin 'yan kason zuwa wasu gidajen wakafin na daban. 

Wata Kungiyar kula da kare hakkin 'yan kaso a vasar ta Venezuwela ta ce a karshen shekara ta 2016 adadin yawan 'yan kason kasar ya kai mutun dubu 88,