1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An shirya zaman taron shawo kan rikicin siyasa

Ramatu Garba Baba
February 7, 2019

A wannan Alhamis, wasu daga cikin kasashen yankin Turai da na Latin Amirka za su yi wani zama na musanman kan nemo hanyar warware rikicin siyasan kasar Venezuela da ya haifar da tsaiko na isar da agaji ga mabukata.

https://p.dw.com/p/3CtRS
Venezuela, Caracas: Demonstrationen
Hoto: picture-alliance/D. Hook

An shirya zaman taron ne, bayan da ake ci gaba da ja-in-ja a tsakanin Shugaba Nicolas Maduro da jagoran Adawa Juan Guaido kan madafun iko. Zaman  zai gudana a birnin Montevideo na kasar Uruguay, don duba hanyar da za a bi don samar da maslaha da kuma damar isar da kayyakin agaji, bayan da aka zargi sojoji da laifin rufe kan iyakar kasar da kasar Kolombiya.

Rikicin shugabanci a Venezuelan, ya raba kan kasashen duniya, inda kasashen Amirka, Faransa da Jamus da Spaniya da Kanada da kuma Ostireliya ke nuna goyon bayansu ga jagoran adawa Juan Guido da ya ayyana kansa a matsayin shugaba na riko, a yayin da Rasha da Chaina ke tsayin daka ga Shugaba Nicolas Maduro.