1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Venezuela: Sojoji na goyon bayan Maduro

Abdullahi Tanko Bala
January 24, 2019

Manyan kwamandojin soji a kasar Venezuela sun jaddada goyon baya ga shugaba Nicolas Maduro wanda ke fuskantar kalubale game da shugabancinsa.

https://p.dw.com/p/3C9Cw
Venezuela Caracas neuer Verteidigungsminister Vladimir Padrino Lopez
Hoto: Getty Images/AFP/L. Robayo

Ministan tsaron kasar Vladimir Padrino Lopez a wani jawabi da ya yi ga 'yan jarida a ranar Alhamis din nan ya yi watsi da dukkan wata barazana ta haifar da tashin hankali a kasar. 
 
Yace muna martaba gwamnatinmu, aikin mu shine tabbatar da zaman lafiya da kare 'yancin cin gashin kan kasarmu. A dangane da haka muna jaddada goyon bayan mu ga shugaban da aka zaba bisa tafarkin kundin tsarin mulkin Venezuela, Nicolas Maduro.

A waje guda dai jagoran adawa Juan Guaido a ranar Laraba ya ayyna kansa a matsayin shugaban rikon kwarya a wani jawabin da ya yiwa dubban magoya bayansa a birnin Caracas tare da kiran gudanar da sabon zabe domin mayar da kasar kan turbar dimukaradiyya. 

Sakataren harkokin wajen Amirka Mike Pompeo ya gargadi Venezuela da cewa kada ta kuskura ta yi amfani da karfin soji akan masu zanga zanga. Yana mai kira ga kasashen duniya su goyi bayan Juan Guaido da ya ayyana kansa shugaban rikon kwarya.