Rikicin Venezuela ya dauki sabon salo
January 24, 2019Bayan matakin ayyana kan nasa a matsayin shugaban kasa na riko, Guaido ya kuma bukaci magoya bayansa su fito kan tituna domin nuna adawarsu da Shugaba Maduro. Tuni dai kasar Amirka ta nuna goyon baya ga wannan yunkuri na Guaido. A nasa bangaren, Shugaba Maduro ya bayyana cewa Guaido da magoya bayansa na kokarin yi masa juyin mulki, inda ya bukaci sojojin kasar da su yi kokarin dawo da doka da oda. Ya kara da cewa gwamnatinsa ta yanke duk wata huldar diplomasiyya da Amirka, tare da bai wa dukkan jami'an diplomasiyyar Amirkan da ke kasar sa'o'i 72 su fice daga Venezuela. Tuni dai jami'an 'yan sanda a Caracas babban birnin kasar, suka yi amfani da hayaki mai sa hawaye da harsasan roba a arangamar da suka yi da 'yan adawa a kan titunan, inda rahotanni ke nunar da cewa mutane 13 ne suka rasa rayukansu a makon da ya gabata.