1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

UNICEF ya ce an sami sauki a auren wuri a duniya

March 6, 2018

Asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya yi marhabin da sabon labarin da ya yi nunin raguwa a auren wuri da ake yi wa mata masu kananan shekaru. Sai dai fa asusun ya ce da sauran rina a kaba.

https://p.dw.com/p/2tme5
Kinder Heirat Minderjährige Mauretanien Jemila Mint Mohamed Lemin Zwangsheirat
Wata yarinyar da ta amarce da kananan shekaruHoto: Jemal Moustapha

Wani rahoton da asusun na UNICEF ya fitar ya ce kokarin da duniya ta yi na wayar da kan jama’a ya taka muhimmiyar rawa wajen rage matsalar auren na wuri ga ‘yan mata kanana da suka kai miliyan 25 a kasashen da ke kudancin nahiyar Asiya, daga shekarar 2008. Sai dai asusun na Majalisar Dinkin Duniya, ya ce in ba an tashi ba, akwai ‘yan mata miliyan 150 da ke kan hadarin shiga wannan tarkon na aure suna kasa da shekaru 18 da haihuwa nan da shekara ta 2030, shekarar da kuwa ake burin ganin an cimma yaki da wannan dabi’a.

Babban dai abin da sabbin alkaluman suka nunar, shi ne a yanzu kashi 15 cikin dari ne saukin da aka samu, daya kenan cikin ‚‘yan mata biyar da ake yi wa yuren na wuri, a shekaru goma da suka gabata. A kasashen kudancin nahiyar Asiya, abin da ya fito fili shi ne ilimantar da kananan ‘yan mata da nasarar fadakar da jama’a da gwamnatoci suka yi, su ne suka taimaka wajen rage miliyoyin wadanda ke shiga tarkon.

Opfer der Zwangsehe Burkina Faso
Hoto: Getty Images/P.Parrot

Akalla dai akwai mata miliyan 650 da aka aurar da su tun suna kanana. 'Yan mata miliyan 12 ne ake yi wa hakan a kowace shekara. A kasashen Afirka kudu da hamadar Sahara alkaluma sun yi nunin cewa a kasar Habasha ne wato Ethiopia aka sami sauki daga cikin kasashe biyar da suka yi kaurin suna a wannan lamari.