1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kira domin sasantawa da 'yan IS

Lateefa Mustapha Ja'afarMarch 13, 2015

Asusun kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya wato UNICEF reshen kasar Siriya ya bukaci da a sasanta da kungiyar 'yan ta'addan IS.

https://p.dw.com/p/1EqR3
PK zu Unicef-Bericht über syrische Kinder
Hoto: picture-alliance/dpa/S. Pilick

Asusun na UNICEF dai ya ce ya yi wannan kira ne domin samun damar kai agaji ga kanana yaran da ke yankunan da suke karkashin IS din. A cewar daya daga cikin mambobin asusun Hanaa Singer dole ne a dauki wannan mataki domin a ceto rayuwar dinbin kananan yaran da ke cinkin garari. Ta shaidawa manema labarai a birnin Geneva cewa sun dade suna bibiyar 'yan IS din domin su basu dama amma sun ki su yi magana da su, tana mai cewa bawai alhakin kungiyoyin bada agaji bane kadai tallafawa wadanda ke cikin taskun ya zama wajibi sauran sassan da ke cikin rikicin su sanya baki. Suma sauran kungiyoyin bada agaji na Majalisar ta Dinkin Duniya sun bayyana cewa suna son kai agaji ga miliyoyin fararen hula da ke cikin halin tasku a yankunan da ke karkashin ikon IS din, sai dai kungiyar ta ki saurarar su.