UNICEF: Rikicin Gabas ta Tsakiya na hallaka yara | Labarai | DW | 05.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

UNICEF: Rikicin Gabas ta Tsakiya na hallaka yara

Fiye da kananan yara 80 ne aka kashe a yankunan da ke fama da tashe-tashen hankula a Gabas ta Tsakiya, musamman kasar Siriya a cikin watan Janairun da ya gabata.

Asusun kula kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya ya ce watan Janairun 2018, ya kasance bakar wata ga kananan yara ganin yadda aka zubda jinin yara a kasasahen Iraki da Siriya da Falatsinu da Yemen da kuma Libiya.

UNICEF ta ce ba za a bari jinin yaran ya bi ruwa ba, wajibi a su taimaka a daga muroyoyin wadanda ba hali su bayyana kukansu. A don haka suke kira da a kawo karshen afkawa kananan yara a lokutan yaki.  

Wasu alkaluma da MDD ta wallafa ya nuna cewa an kashe kananan yara 59 a Siriya, yayin da kasar Yemen ke biyemata cikin kashen da akafi salwantar da rayuwar yara.