Ana tuhumar tsohon gwamnan babban bankin Lebanon
September 9, 2024Wani alkali a kasar Lebanon ya ba da umurnin cafke tsohon gwamnan babban bankin kasar Riad Salameh bisa tuhumar da ake masa na almubazzaranci lokacin da yake jagorancin babban bankin.
Shi dai Salameh mai shekaru 75 da haihuwa yana fuskantar tuhume-tuhume da dama a kimanin shekaru 30 da ya kwashe yana jagorancin babban bankin kasar ta Lebanon, da suka hada da almubazzaranci da halarta kudin haram da kauce wa biyan haraji.
Tun shekarar da ta gabata kasashen Amurka da Birtaniya gami da Kanada suka bayyana saka takunkumi kan Riad Salameh tsohon gwamnan babban bakin kasar ta Lebanon saboda zargin samun hannunsa wajen halarta kudin haram. Sai dai Salameh ya musanta duk zargin aikata wani laifi inda ya ce ya samu arzikinsa ne daga hannun jari da ya zuba tare da 'yan kasuwa masu zaman kansu.