1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikici ya ritsa da wasu 'yan jarida

December 27, 2020

An jikkata 'yan jarida biyu tare da rasa rai yayin wata arangamar jami'an tsaro da magoya bayan Bobi Wine a Uganda.

https://p.dw.com/p/3nGQe
Uganda Festnahme Robert Kyagulanyi aka Bobi Wine
Hoto: Abubaker Lubowa/REUTERS

'Yan sanda a Birnin Kampala fadar gwamnatin Yuganda, sun yi amfani da karfin tuwo wajen tarwatsa wani gangamin magoya bayan mawakin nan kuma dan majalisar kasar Bobo Wine.

Arangamar dai ta yi sanadiyyar hallaka wani mai tsaron lafiyar dan majalisar, tare da jikkata wasu 'yan jarida 2 wadanda yanzu suna asibitin babban birnin inda suke karbar magani.

A ranar Asabar din da ta gabata ne hukumar zaben kasar ta bayar da sanarwar tsaida duk wani kamfe, wanda ake ganin hakan ne ya sa 'yan sandan suka farwa taron.

Bobi Wine ya kasance dan adawan da ke kan gaba wajen kalubalantar shugaba Yuweri Museveni, wanda ke jagorancin kasar tun a shekara ta 1986.