1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ukraine na samun nasara a yankin Kherson

Binta Aliyu Zurmi
October 6, 2022

Shugaba Zelensky ya tabbatar da sake karbe ikon wasu yankunan Kherson da ke kudancin kasar da Rasha ta yi bikin shigar da su a cikin kasarta a makon da a gabata.

https://p.dw.com/p/4HolX
Ukraine Präsident Zelenskiy
Hoto: Valentyn Ogirenk/REUTERS

A jawabinsa na duk dare ga 'yan kasar, shugaba Zelensky ya ce, yankunan da aka kwato galibi suna kudu maso gabashin Kherson ne da suka hada da Novovoskresenske da Novohryhorivka da kuma Petropavlivka

A jiya Laraba shugaba Vladmir Putin ya saka hannu a hukumance, inda yankunan Ukraine 4 suka koma cikin kasar sa, hakan na nufin kaso 18 cikin dari na yankin kasar Ukraine ya koma ga Rasha.

Kasashen yamma da Majalisar Dinkin Duniya sun yi tir da wannan mataki, inda a gaba za su kada kuri'a a hukumance da na kin amincewa da hakan, sai dai mahukunta a Rasha na neman a gudanar da zaben a asirce.