Ukraine ta janye mafi yawan sojojinta daga Debaltseve | Labarai | DW | 18.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ukraine ta janye mafi yawan sojojinta daga Debaltseve

Shugaba Poroshenko na Ukraine ya tabbatar da fara janye sojojin gwamnati daga filin daga na garin Debaltseve.

Shugaban Ukraine Petro Poroshenko ya tabbatar da fara janye dakarun gwamnati daga garin Debaltseve inda ake gwabza kazamin fada. Shugaban ya fada a birnin Kiev cewa cikin kyakkyawan tsari kashi daya cikin biyar na sojojin sun janye daga yankin mai muhimmanci. Shi ma kakakin sojin kasar Andriy Lysenko ya tabbatar cewa yanzu haka kashi 80 cikin 100 na dakarun gwamnati sun fice daga garin.

"A wannan Laraba rundunar sojin Ukraine ta kaddamar da wani ingantaccen tsarin janye dakarun da ke aikin yaki da ta'addanci daga garin Debaltseve. Yanzu haka kusan kashi 80 cikin 100 na sojojin Ukraine sun bar yankin, za a kuma kammala wannan janyewar nan gaba kadan."

A ranar Talata 'yan aware masu goyon bayan Rasha sun karbi iko da wasu hanyoyin sufuri masu muhimmanci a garin. Kungiyar EU ta yi tir da farmakin da 'yan tawaye suka kai da cewa ya saba wa yarjejeniyar tsagaita wuta.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu