Ukraine ta ce wasu tankokin yakin Rasha sun tsallake iyakokinta | Labarai | DW | 25.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ukraine ta ce wasu tankokin yakin Rasha sun tsallake iyakokinta

Hakan na zuwa ne yayin da gwamnati a birnin Mosko ta ba da sanarwar shirin tura ayarin motocin kayan agaji karo na biyu zuwa gabashin Ukraine.

Sojojin Ukraine sun ce suna fafatawa da wani ayarin motocin sulke daga Rasha a kusa da birnin Mariupol. Rundunar soji ta ce motocin yakin daga Rasha sun tsallake kan iyakokin Ukraine amma an taka musu biriki. Wani kakakin rundunar ya ce har yanzu ana gwabza fada. A kuma halin da ake ciki Rasha ta sanar cewa za ta sake tura motocin kayan agaji ga yankunan da ake fada ciki na gabashin Ukraine. Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya ce tuni an sanar da gwamnatin Ukraine game da wannan sabon yunkurin daga Rasha, wadda duk da sukar da ta sha da farko game da tura ayarin manyan motocin kayan agaji, yanzu kuma ke shirin kai agajin a 'yan kwanaki masu zuwa.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Abdourahamane Hassane