1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ukraine ta ce ba za ta bari Kirimiya ta kubuce mata ba

March 8, 2014

Mahukuntan Ukraine sun ce za su yi bakin kokarinsu wajen ganin yankin Kirimya da suke takkadama kansa da kasar Rasha bai kubuce daga hannunsu ba.

https://p.dw.com/p/1BMAT
Ukraine Krim Simferopol Parlament besetzt Flagge
Hoto: Reuters

Ministan harkokin wajen Ukraine din na rikon kwarya ya ambata hakan a wannan Asabar din, inda ya kara da cewar yankin na karkashin Ukraine kuma zai cigaba da kasancewar karkashin kulawarta sannan gwamnatinsu ba za ta bari wajen ya fada hannun kowacce kasa ba.

A wani labarin kuma, gwamnatin Rasha ta ce za ta hana dukannin wani aiki da ake yi na sanya idanu kan makamanta muddin aka cigaba da yi mata baraza saboda matsayin da ta dauka kan yankin Kirimiya wanda suke takaddama kansa da kasar Ukraine.

Fadar mulki ta Kremlin dai ta ce ta dau wannan mataki ne saboda barazanar da ake cigaba da yi mata da ma zarge-zargen da ta ke fuskanta daga yammacin duniya wandanda ta ce ba su da tushe bare makama.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Usman Shehu Usman