1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ukraine na zargin Rasha da kutse

August 28, 2014

Kwana guda bayan ganawa tsakanin shugaban kasar Ukraine Petro Poroshenko da takwaransa na Rasha Vladmir Putin, mahukuntan Kiev sun zargi Moscow da yin kutse.

https://p.dw.com/p/1D3A2
Hoto: picture alliance/AP Photo

Ma'aikatar tsaro ta Ukraine din ce ta tabbatar da kutsen da dakarun Rashan suka yi domin taimakwa 'yan aware masu goyon bayan Moscow inda ta ce yanzu haka garin Novoazovs da ke kan iyakar kasashen biyu da kuma wasu yankuna a kudu maso gabashin Ukraine na hannu dakarun Rashan da kuma 'yan awaren kasar. Tuni dai mahukuntan Moscow suka musanta wannan batu kamar yadda suka saba, suna masu cewa Rasha bata taba baiwa 'yan awaren tallafin kayan yaki ba. Yayin ganawar shugabannin kasashen biyu a birnin Minsk wadda itace ta farko Shugaba Poroshenko na Ukraine ya ce Kiev za ta shirya hanyoyin da za a bi wajen zama kan teburin sulhu da 'yan awaren.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Umaru Aliyu