1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ukraine na son Jamus ta matsa wa Rasha lamba

Yusuf BalaJanuary 8, 2015

A ziyararsa ta kwanaki biyu a Jamus firaministan Ukraine Arseniy Yatsenyuk na kokarin ganin Angela Merkel ta mara baya a kara matsa kaimi wajen karya tattalin arzikin Rasha.

https://p.dw.com/p/1EGm0
Symbolbild Ukraine - Milliardenhilfen zugesagt Jazenjuk und Merkel
Hoto: Reuters/Hannibal Hanschke

Firaminstan kasar Ukraine ya gana da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel a yau Alhamis, inda ya nanata bukatarsa ta ganin ta kara kafewa kan batun ci gaban takunkumin karya tattalin arziki ga kasar Rasha, a yayin taron tattaunawa kan rikicin Ukraine da shugaba Vladimir Putin a mako mai kamawa.

Arseniy Yatsenyuk na ziyarar zuwa wannan babbar kasa cikin kasashen Kungiyar Tarayyar Turai mai mambobi 28 gabanin sake matsaya kan shirin karya tattalin arzikin kasar ta Rasha wacce tuni abin ke shafar dukkanin bangarorin biyu.

Jawaban da ke fiitowa daga bangaren makusantan shugaba Merkel da shugaba Francois Hollande na Faransa na nuni da cewa, mahukuntan biyu na duba watanni biyu na abubuwan da suka faru kan rikicin na Ukraine inda za su duba yiwuwar yin sassauci ko akasin haka kan kasar ta Rasha.